By Abbas Yakubu Yaura
Wani dalibi dan shekara 20 mai suna Yakubu Muhammed a ranar Talata ya bayyana a gaban wata kotun karamar hukumar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja bisa zarginsa da yunkurin barazanar kashe makwabtansa.
DUBA WANNAN LABARIN: Korar ‘Yan Majalisa: ‘Yan Sanda Sun Mamaye Harabar Ƙofar Shiga Majalissar Dokokin Cross River
Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Muhammed wanda ke zaune a kauyen Giri Kposere, Gwagwalada da laifin zamba, tsoratarwa da kuma cin zarafi.
Lauyan masu shigar da kara, Abdullahi Tanko ya shaida wa kotun cewa Ms Victoria Adegbola, wacce ke zaune a kauyen Giri Gauta Gwagwalada ta kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda a ranar Litinin.
Tanko ya ce wanda ake kara ana zargin sa da laifin shiga harabar gidan mahaifin mai karar inda ya ci zarafinta da ita da mahaifinta.
Ya ce wanda ake tuhumar ya kuma yi barazanar kashe su duka.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 342, 397 da 264 na kundin laifuffuka.
Wanda ake tuhumar ya musanta zargin aikata laifin.
Lauyan da ke kare wadanda ake kara Hussein Isah, ya roki kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa bisa tanadin sashe na 158 da 162 na dokar shari’a ta ACJA don dakile ikirarin da ya yi na neman beli.
Isah ya ce wanda ake kara idan har aka bayar da belin ba zai yi tsallen bada belin ba, kuma zai kasance a gaban kotu har sai an yanke hukunci.
Ya roki kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa cikin mafi sassaucin ra’ayi.
Mai shari’a Sani Umar, ya shigar da karar wanda ake tuhumar da bayar da belinsa a kan kudi Naira 300,000 tare da tsayayyen mutum daya wanda zai tsaya masa .
Alkalin kotun ya ce idan wanda ake kara ya gaza cika sharuddan belin, za a ci gaba da tsare shi a gidan yari na Najeriya da ke Suleja.
Alkalin ya dage sauraron karar har zuwa ranar 18 ga watan Mayu domin cigaba da sauraren karar. (NAN)