By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa wani gini mai hawa daya ya ruguje a unguwar Dorayi Ciranci Layin Makabarta dake jihar kano.
Tunda farko dai wata mata mai suna Binta Sa’idu itace wacce ta kira jami’an hukumar kashe gobara ta jihar kano dan kawo musu a gajin gaggawa dan kubutar da mutanen dake cikin gidan.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar kano Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar mana da faruwa lamarin inda yace hatsarin ya rutsa da wata mata mai suna Aisha Zubairu mai shekaru 40 da kuma Rumaisa Zakariya mai shekaru 3.
Kazalika yace lamarin ya afku da misalin 8:25 na dare inda su kuma jami’an su suka isa wajen da misalin karfe 8:31 na dare dan kai agaji.
Yusuf yace anyi nasara kubutar dasu basa cikin hayyacin su kuma jami’ansu sun kaisu asibitin kwararru na Murtala dan basu kulawar likitoci.