- Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, a ranar Juma’a, ya dakatar da dukkan shugabannin kananan hukumomi da kansilolinsu
- Majalisar dokokin jihar a ranar Larabar da ta gabata ta ba gwamnan shawarar dakatar da kafatanin shugabannin kananan hukumomin jihar
- Wasikar ta umurci kafatanin shugabannin kananan hukumomin da su mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a ranar Juma’a, ya dakatar da dukkan shugabannin kananan hukumomi 23 da kansilolinsu, Punch ta rawaito.
Babban Sakataren ofishin kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu, Ode Ochelle, ya bayyana hakan a wata takarda mai dauke da kwanan watan 23 ga watan Yuni, 2023.
KARANTA WANNAN: An Tuhumi Wasu Yara 3 Da Laifin Hallaka Wani Dawisu Da Kudin Sa Ya Kai Miliyan N1m
Sanarwar ta kuma bayyana dakatar da dukkan shugabannin kananan hukumomi 23 da shugabannin majalisun guda 23.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa majalisar dokokin jihar a ranar Larabar da ta gabata ta ba gwamnan shawarar dakatar da kafatanin shugabannin kananan hukumomin jihar.
Majalisar a zamanta ta yanke shawarar dakatar da bangaren zartarwa da na majalisa na mataki na uku na gwamnatin jihar.
“Domin gudanar da bitar ba tare da tsangwama ba, kwamitin ya ba da shawarar dakatar da shugabannin majalisar zartarwa a dukkanin kananan hukumomi 23 domin hada kai da majalisun zartaswa don yin almundahana da dukiyar al’umma da aka amince da su,” inji shi.
Wasikar ta kara da cewa, “Bayan amincewar Gwamnan Jihar Binuwai, Rev Fr Hyacinth Alia, kan matakin da Majalisar Dokokin Jihar Binuwai ta dauka na dakatar da ku da daukacin shugabannin kananan hukumomin daga ofis kamar yadda ya ke kunshe a cikin wata wasika daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, mai lamaba CAB/BS/SSG/ADM/35/T/XX mai kwanan wata 23 ga watan Yuni 2023.
“An umurce ku da ku ci gaba da kasancewa a dakace ba tare da bata lokaci ba.
Wasikar ta umurci dukkan shugabannin da su mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu ga daraktan ma’aikata da gudanarwa da kuma magatakardar majalisar.
A wani labarin kuma, Babu Wani Ɗan Filato da Zai Kara Jikkata Sanadiyyar Rikici – Gwamna Mutfwang
Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato a ranar Juma’a ya tabbatar wa mazauna jihar cewa babu wani wanda za’a sake cin zarafinsa biyo bayan tsarin mulkin kwamitin da zai duba aikin nadin ma’aikatan jihar da aka yi kwanan nan.
DAILY POST ta tuna cewa a baya-bayan nan ne Gwamna Mutfwang ya dakatar da duk ma’aikata wadanda suka yi aiki tun watan Oktoban shekarar da ta gabata da gwamnatin da ta shude ta Simon Lalong sakamakon rashin jituwar da aka samu a aikin.