Mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum daya a yankin Akungba-Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma a jihar Ondo.
Hadarin wanda ya afku a ranar Talata a kan titin Ikare da Akungba ya faru ne sakamakon wani direban tirela da ke jigilar kayan abinci wanda ya kasa shawo kan matsalar birki.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a jihar, Ezekiel Sonallah ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho.
Ya ce mutane 10 da suka hada da maza tara da mace daya ne suka yi hatsarin.
Kwamandan sashin ya kuma gargadi masu ababen hawa da su tabbatar da cewa motocinsu suna cikin koshin lafiya kafin su fara kowace tafiya.
An ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa, yayin da wadanda suka jikkata ke karbar kulawa a babban asibitin garin Ikare-Akoko.