Wani dan kasuwa mai shekaru 34, Cyprian Ebenezer, a ranar Litinin ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Ikeja, Legas, bisa zarginsa da raunata matarsa da adda.
‘Yan sanda sun tuhumi Ebenezer, wanda ke zaune a Oke-Odo, Legas, da laifin kai hari tare da haddasa munanan raunuka a jikin matar sa.
Lauyan mai shigar da kara, DSP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Afrilu a adireshin da aka ambata a sama.
Ta yi zargin cewa wanda ake kara da misalin karfe 11:30 na dare ya lakadawa matar tasa Ruth duka a ido.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce wanda ake tuhumar ya yi amfani da adda a kan matarsa, inda ya yi mata munanan raunuka a jikinta.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 173 da 245 na dokokin aikata laifuka na jihar Legas, na shekarar 2015.
Wanda ake tuhumar ya musanta zargin aikata laifin.
Alkalin kotun Majistare Ejiro Kubeinje ya danka wanda ake tuhumar a hannun beli a kan kudi Naira 100,000 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.
Alkalin kotun ya bada umarnin cewa wadanda za su tsaya masa dole ne su kasance da shaidar biyan haraji, a tantance adireshi sannan daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya zama makusancin sa na jini.
Kubeinje ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 31 ga watan Mayu domin cigaba da sauraren karar.
(NAN)