A ranar Larabar da ta gabata ne wani magidanci mai suna Issele-Uku da ke karamar hukumar Aniocha ta Arewa a jihar Delta ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade.
Jaridar Daily Independent ta bayyana cewa wacce abin ya shafa ta mutu sa’o’i kadan bayan faruwar lamarin a asibitin El Comfort da ke Bonsaac a Asaba.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya da ta yi magana da wani shaida a boye ya ce, wacce aka kashe ta bayyana cewa an kai ta wani otal da ke Issele-Uku inda anan ne ake zargin an yi mata fyade.
A cewar majiyar da ta ki bayyana sunan wacce aka kashe din, ta ce wadda ake zargin ya yi amfani da farar takarda wajen goge jinin da ke cikin al’aurar ta.
Majiyar ta kuma bayyana cewa wanda ake zargin direban mota ne a wata cibiyar Gwamnati, inda ya kara da cewa yana da mata da yara biyu.
Majiyar ta ce “Wannan shi ne zargin fyade na biyu da aka samu a Issele-Uku a ‘yan kwanakin nan”.
A halin da ake ciki kuma, an ajiye gawarwakin wadanda aka kashe a cibiyar lafiya ta tarayya, FMC, dakin ajiye gawa dake garin Asaba.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, PPRO a jihar, DSP Bright Edafe bai iya tabbatar da faruwar lamarin ba, ya kara da cewa; “Idan wannan lamarin ya faru, toh kwata-kwata, ba a kai rahoto ba, don haka ba zan iya tabbatarwa ba. “
Comments 1