By Abbas Yakubu Yaura
Wasu rahotanni na nuni da cewa an harbe wata matar aure mai suna Salamatu a lokacin da masu garkuwa da mutane suka kai hari a unguwar Piri dake karamar hukumar Kwali a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane takwas ne suka sace inda aka yi garkuwa da su a lamarin wanda ya faru tsakanin Talata zuwa Laraba.
Wani mazaunin garin Yakubu Saidu yace masu garkuwa da mutanen sun fara kai farmaki gidaje biyu inda suka yi awon gaba da wasu mutane biyu yayin da ake ta harbe-harbe.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Masu garkuwa da mutanen sun far wa wani dillalin sayar da mota mai suna Sadauna amma da yake ba su same shi ba, sai suka tafi tare da wasu ‘yan uwansa guda biyu a daren ranar Talata.
Sannan an ce sun sake dawowa cikin garin da al’ummar suke ne a ranar Laraba lokacin da aka kashe Salamatu.
Marigayiyar, wadda babbar matar Yusuf Maigunwa, dillalin doya ce a garin Kwali, ta yi yunkurin tserewa ne ta kofar baya a lokacin da aka harbe ta.
“Mijin marigayiyar yana gida lokacin da masu garkuwar suka zo, amma ba su iya gano inda yake boye ba, yayin da suka tafi da matarsa ta biyu da wasu mutane biyu a cikin gidan,” inji shi.
Ya kara da cewa wasu gungun masu garkuwa da mutane da suka sanya kansu a wurare masu mahimmanci a cikin al’umma, sun mamaye gidaje biyu tare da yi wa mazauna garin uku bulala.
Ya ce an yi jana’izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, bai amsa kiran waya ko amsa sakon da aka aike mata don tabbatar da faruwar lamarin ba.