By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar tsaro ta farin kaya ta jihar Kwara ta kama wani mai gadi mai suna Jacob Obomerelu mai shekaru 47 bisa zargin yi wa diyarsa mai shekaru 18 fyade.
Obomerelu, wanda yake aiki a matsayin mai gadi a wani gini dake kan titin Awolowo, unguwar Tanke, Ilorin, ana zarginsa da yiwa ‘yarsa ta cikinsa fyade a wani gidan wanda kuma ya zama gidansa ne.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 6 ga watan Disamba, 2021.
Matashiyar wadda lamarin ya shafa ta bar gidan mahaifinta a shekarar 2017 bayan rabuwa da mahaifiyarta, wata mai suna Alhaja Mariam Bello ta dauke ta a unguwar Gaa-Akanbi dake Ilorin.
Matashiyar ta koma wurin mahaifinta ne bayan sun samu rashin fahimta da mahaifiyar ta.
Jaridar PUNCH tattaro cewa Obomerelu yayi mata fyade a daren farko data zauna a gidansa tare da shi.
“Tace ta roke shi da kada ya yi mata fyade, amma duk rokon data yi masa ya tashi abanza inda yayi kunnen uwar shegu yaki sauraronta, domin ya kasance kamar wanda aka yi masa sata, sannan ya ba ta Naira 1,000 domin ta siyo maganin da zai gusar mata hankali,” in ji sanarwar NSCDC.
Kakakin hukumar a jihar, Babawale Afolabi, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya ce ya faru ne a wurin aikin wanda ake zargin.
Babawale yace, “A ranar Talata, 7 ga watan Disamba, 2021, wata mata mai suna Alhaja Mariam Bello ta sanar da mu, inda tace yarinyar wacce ta kasance ‘yar goyon tace mahaifinta ya yi mata fyade, ta kara da cewa wanda iftila’in ya rutsa da ita mahaifin nata ya saba yi.sannan suna zaune da ita a gidansu dake Isale Gaa Akanbi amma ta koma zama da mahaifinta bayan wata ‘yar rashin fahimta tsakaninta da wanda lamarin ya shafa”
Yace Obomerelu, mai ‘ya’ya hudu daga jihar Edo, ya amsa laifinsa, amma ya dora laifin cewa sharrin shaidan ne, inda ya ce ba ya cikin hayyacinsa lokacin daya aikata hakan.
Babawale ya ce Kwamandan NSCDC na jihar, Mista Iskilu Makinde, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin tare da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.