Wani mai gadi da yake aiki da Polytechnic ta Jahar Osun Iree ya harbe wani Manomie a Eripa, Ƙaramar Hukumar Boluwaduro ta Jahar Osun.
Lamarin ya faru a cikin karshen hutu a yankin Odo-Ada dake a cikin garin.
Mutumen mai Tiv yana tare da ƴan uwanshi bayan yayi aiki daya taso daga garin, Iree ya kashe shi da bindiga.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya Ta Fice Daga Gasar Wasan AFCON Da Ci 1-0 A Hannun Tunisia
Majiyar mu tace wanda ake zargin yayi kisan, ya shiga gona tare da satar doya daga gonar mutumen, inda a tunanin sa mai gonar ya tafi gida.
A lokacin daya lura cewa, mai gonar yana cikin ta da abokanan sa, ya buƙace su dasu tafi gida.
Abun baƙin ciki, bayan ya tafi gida, sai ya lura dacewa ya manta wasu abubuwa a gonar, wanda ya sanya ya koma gonar, amma yana zuwa sai ya tarar wani na satar mashi kayan amfanin gona.
Manomin wanda yana tare da ƴan uwan sa, ya ƙalubalanci wanda yake tonar mashi kayayyakin amfanin gona, inda anan take ya harbe shi ya gudu.