By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da ’ya’ya mata biyu na wani malami a Kwalejin Fasaha ta Tarayya dake Gusau a ranar Juma’a a jihar Zamfara.
An shaida wa manema labarai cewa an yi garkuwa da matar, Binta Umar Jabaka da ‘ya’yan mata biyu, Maryam Abdurrazak da Hafsat Abdurrazak a gidansu da ke unguwar Mareri da misalin karfe 1 na dare.
Wani ma’aikacin kwalejin, Mohammad Lawal, ya ce ‘yan bindigar sun samu shiga gidansu da nufin yin garkuwa da malamin.
A cewarsa,” sun shafe awa daya suna binciken gidan amma malamin ya boye a cikin silin. “
‘Yan bindigar sun tsallake katanga suka shiga gidan Dakta Abdurrazak domin su yi garkuwa da shi amma ya tsere ta silin.
“Sun shafe sama da awa daya suna binciken gidan suna nemansa, amma da ba su same shi ba, sai suka yi awon gaba da matarsa, Binta da ‘ya’yansa mata guda biyu, Maryam da Hafsat.”
‘Yan bindigan sun kira Dakta Abdurrazak da yammacin ranar juma’a, suka shaida masa cewa suna rike da matarsa da ‘ya’yansa guda biyu. Sai dai kuma ba su gaya masa cewa ga adadin kudin da zai biya a matsayin kudin fansa ba.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Tun daga nan ne rundunar ta shirya jami’anta na dabara don bibiyar ‘yan bindigar domin ceto wadanda abin ya shafa,” in ji shi.