Wani Malamin Islamiyya mai suna Alfa Moshood ya sumar da wani dalibin shi zallar bugu bayan da ya zarge shi da sace Mishi Dorina.
Sai dai bayan wannan aika-aika Mallamin tuni ya tsere, lokacin da ya ji cewa labari ya isa ofishin hukumar kare hakkin Bil’adama ta Jihar Kwara.
Dalibin dan shekara 14 wanda ba a bayyana sunan shi ba, bayan farfadowar shi ya bayyana cewa Malamin ya mishi dan banzar duka gabannin sake mika shi ga wasu mutane sittin dake kewaye da su inda kowannen su ya yi mishi bulala goma-goma, inda sai dai ya kusa mutuwa.
Ya kara da cewa bulalar an yi mishi bayan da aka ɗaure sgi a jikin wani teburi a harabar Makarantar.
Shi dai wannan yaro a faɗin shi, Mahaifiyar shi mai suna Ajara ita ce ta sanya shi a wannan Makaranta shekara guda da ta gabata.
Wani Jami’in Hukumar Kare hakkin Bil’adama ta Jihar, ya bayyana wa manema labarai cewa a yanzu haka yaron yana kwance a wani asibiti dake birnin Ilori, yayin da kuma ake ci gaba da farautar Mallamin ruwa a jallo.