Wani matashi mai shekara 32 a duniya, Serif Zorba, ya shiga hannun hukuma bayan ya cakawa wani limami wuƙa a wani masallaci da ke a birnin New Jersey na ƙasar Amurka.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Afrilun 2023.
An cafke Serif Zorba ne bisa zargin cakawa Imam Sayed Elnakib, limamin masallacin Omar a Paterson, cikin New Jersey.
KU KARANTA KUMA: Tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa ya shaƙi iskar ƴanci
A cewar kakakin masallacin, Abdul Hamdan, an cakawa Elnakib, wuƙar ne lokacin Sallah Asuba da misalin ƙarfe 5:30 yayin ruku’u.
Wani bidiyo da aka saki wanda ya ɗauki yadda lamarin ya kasance ya nuna masallatan cikin sahu biyar.
A lokacin da suka ɗuka yin ruku’u, wani mutum mai sanye da rigar sanyi wanda yake a sahu na uku, sai ya ratso cikin masallatan ya cakawa limamin wuƙa ta baya.
Nan da nan masallatan suka yo kan maharin yayin da yayi ƙoƙarin guduwa daga masallacin.
Ana tuhumar Zorba da laifin yunƙurin kisan kai, mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da kuma laifin mallakar makami mai cutarwa.
Lokacin da zai kwashe a gidan kurkuku bisa laifukan da ake tuhumar sa da su zasu kai shekara 26 a gidan gyaran hali.
Abin Takaici: Bayan Kwashe Shekaru Tare, Magidanci Ya Gano ‘Ya’Yansa 2 Ba Na Shi Bane
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya shiga damuwa bayan gano cewa yaran sa 2 ba ƴaƴan sa bane.
Wani mutum mai suna Morris ya shiga cikin takaici bayan ya gano cewa ba shi bane mahaifin yaran sa guda biyu ba da matarsa ta ce ƴaƴan sa ne.
Mai shari’a Lauren Lake ta kotun US Paternity, itace ta bayyana hakan yayin da take yanke hukunci akan ƙarar Morris da matarsa,Thorpe, dangane da ƴaƴan su.