Wani matashi ɗan Najeriya, @niceprince114, yayi wani ɗan ƙaramin bidiyo domin nuna cika alƙawarin da ya yiwa iyayen sa.
A farkon bidiyon ya nuna yadda gidan yake kafin ya fara aikin sauya masa fasali zuwa na zamani. Gidan duk a yamutse yake sannan ko shafe ba ayi ba a bangwayen ginin. Rahoton Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Peter Obi ya magantu kan laƙanin Yes Daddy
Ya ɗauko ma’aikata domin ƙayata gidan. Sannan kafintoci kuma suka sauya tsofaffin kwanon rufin gidan da sababbi. Maɗaukan dake gidan suma sai da aka sake musu fasali.
Lokacin da aka kammala gyaran, mutane da dama sun yaba masa ta yadda ya tuna da iyayen sa bayan ya samu dukiya.
Mahaifiyar sa har rawar murna ta taka a wani bidiyo daban da ya sanya.
Ku kalli bidiyon a nan
Bidiyon ya yaɗu sosai inda ya samu sharhi daga wajen mutane sama da dubu biyu, yayin da sama da mutum dubu talatin suka danna masa alamar ‘like’.
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@omodano ya rubuta:
“Ka bar gida domin ka sanya su farin ciki. Ina taya ka murna. Shin kwana nawa gyaran ya ɗauka?”
@remedyfx1 ya rubuta:
“Kai gwarzon namiji ne. Ka fifita iyayenka.”
@user9874160966197 ya rubuta:
“Ina taya ka murna, fatan ƙara samun buɗi.”
@AYODEJI _KK _NASH04 ya rubuta:
“Ina taya ka murna ka sanya iyayen ka farin ciki”