By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an ‘yan sandan da ke aiki da sashin ofishin Ajegunle reshen jihar Legas sun kama wani mutum mai shekaru 34 mai suna Godwin Iroro bisa laifin lalata da ‘yar abokinsa mai shekaru 10 wadda an sakaya sunanta.
An kama wanda ake zargin a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2021, inda yace sharrin shaidan ne yasa shi aikata laifin.
An kama Iroro ne biyo bayan korafin da mahaifin wanda abin ya shafa, Chukwudi Chime ya kai ofishin ‘yan sanda, wanda ya lura da yadda ‘yar tasa ke tafiya cikin wani yana yi na mamaki inda daga baya yasan abin da ya faru da ita.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Adekunle Ajisebutu, a wata sanarwa da ya fitar yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa amma ya zargi cewa shaidan ne ya sashi aikata laifin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanarwar mai suna, ‘Mutum mai shekaru 34, ya yi lalata da ‘yar abokinsa ‘yar shekara 10.
“Wanda ake zargin, da aka yi masa tambayoyi, ya amsa laifinsa amma ya dora laifin a kan shaidan. Sannan ya kuma yi ikirarin cewa ya yi lalata da karamar yarinyar sau biyu kacal kafin asirinsa ya tonu
kwamishinan ‘yan sanda, CP Hakeem Odumosu, nan take ya bada umarnin a mika shi sashin kula da jinsi na rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike mai zurfi da kuma tuhumar shi.