Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu Sanata Ibrahim Danbaba ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Danbaba ya bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ne a wata wasika da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta, yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Dan majalisar ya ce ya bar PDP ne saboda rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar reshen jihar Sokoto, kamar yadda ya rubuta a wasikar ficewar ta sa.
Ya ce akidar APC ta yi daidai da amannarsa na siyasa.
A wani labarin Kuma na daban.
Jami’an Yan sanda sun kama wani matashi Mai halin Bera a otel-otel na jihar Oyo
Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, a ranar Talata, ta kama wani barawo Dan shekaru 23, Mai suna Bankole Mustapha, a wani otal da ke unguwar Bodija a Ibadan, babban birnin jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, wanda ya gabatar da wanda ake zargin a Ibadan, ya ce ya kware wajen siga cikin otal-otal da sauran wuraren shakatawa a Ibadan domin yin ta
Olafeso ya ce, “A kokarin da ake yi na ganin an kawar da marasa kishin jihar Oyo, jami’an rundunar ‘yan sandan reshen Bodija Housing Division, a yayin da suke aikin leken asiri a yankin Bodija/Sango da ke karamar hukumar Ibadan ta Arewa a ranar Litinin, 25 ga watan Janairu. , 2022, da misalin karfe 0100 na safe, an kama wani mutum Mai suna Bankole Mustapha ‘mai shekaru 23, Wanda dan fashi ne da ya kware wajen sata a otal-otal da sauran wuraren shakatawa.
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya tunkari wani ma’aikacin otal din ne da yammacin ranar Lahadin da sunan cewa shi magidanci ne, inda ya tsara wata muguwar hanya ta aiwatar da shirinsa na kwashe kayayyaki daga otal din ta hanyar neman wani daki da ke kusa da hanyar fita otal din.
“A ci gaba da aikin nasa, da misalin karfe 0100 na safe, ya tafi da talabijin kirar Kamfanin Samsung mai inci 32 da ke cikin dakinsa da kuma wani talabijin mara alama mai girman inci 32 a wurin liyafar.”