By Abbas Yakubu Yaura
An gurfanar da wani tela mai shekaru 29, Gado Yahaya a gaban wata kotun majistare da ke Kaduna a ranar Litinin, bisa zarginsa da kashe makwabcinsa a wani rikici da ya barke kan bokitin ruwa a yankin Rigasa ta jihar.
A cewar wani mazaunin garin Rigasa, Yahaya ya yi fada da Liman Salisu ne a lokacin da suke takaddama kan bokitin ruwa wanda ya yi sanadin mutuwar Salisu.
“Mutumin mazaunin Rigasa dake jihar Kaduna an kuma gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare da ke Kaduna a ranar Litinin da ta gabata bisa tuhumarsa da laifin kisan kai.”
“Mai gabatar da kara, Insp.Chidi Leo ya yi zargin cewa Yahaya ya kashe Salisu ne da wata baraka a fafatawar da suka yi kan bokitin ruwa.
“A cikin fadan, sai ya shiga kicin, ya dauko kwarkwasa ya buga a kan Salisu, inda ya fadi nan take bayan an buge shi a kai kuma ya mutu a hanyar zuwa asibiti.”
Lauyan mai gabatar da kara ya ce Yahaya ya rubuta kuma ya sanya hannu kan wata takardar shaida lokacin da aka kawo shi ofishin ‘yan sanda domin yi masa tambayoyi.
Ya kara da cewa laifin ya ci karo da tanadin sashe na 190 na kundin laifuffuka na jihar Kaduna shekarar 2017.
Sai dai kotun ta umurci ‘yan sanda da su mika takardar karar zuwa daraktan kararrakin jama’a na Jiha don neman shawarar shari’a sannan ta dage karar zuwa ranar 9 ga watan Maris, 2022.
Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya bayar da umarnin a tasa keyar Yahaya zuwa gidan gyaran hali, kuma ya ki amsa rokonsa bisa dalilin da ya sa kotu ba ta da hurumin sauraron karar.