Ana Zargin wani Ba’amurke a jihar Florida mai suna Zachary Moncada, da harbin makwabcinsa yayin da suke takaddama kan kade-kade da a ranar jajibirin Kirsimeti.
Jaridar CBS 12 ta ruwaito cewa, an zargi matashin mai shekaru 31 da harbin mutumin a baya kafin ‘yan uwan wanda abin ya shafa su kama shi a gaban kofar gidansu na Boca Raton.
Iyalan wanda aka kashe sun kwance bindigar dake hannun Moncada, amma an sake Jin karar harbe-harb yayin fafatawar kafin ‘yan sanda su isa.
Sai dai har kawo hada wannan rahoton ba a faiyace wanda ya kunna waƙar ba a tsakanin mutanen biyu.
An kwantar da wanda aka harba a wani asibiti, in ji NY Post.
An kama Moncada kuma an tuhume shi da yunkurin kisan kai a matakin farko, da kuma Kai mummuna hari.