A wannan dare na Talata za a fafata wasannin mako na uku na gasar zakarun nahiyar turai tsakanin ƙungiyiyin ƙwallon ƙafa da dama.
Ga jerin wasannin na yau kamar haka:
F/C Porto da Marseille.
Manchester City da Olympiakos.
Shakhtar da Brussia M’gladbach.
Real Madrid da Inter Milan.
Atalanta da Liverpool.
Midtjylland da Ajax.
Salzburg da Bayern Munich
Lokomotiv Moscow da Athletico Madrid.
A shekarar data gabata dai Bayern Munich ce ta zamo zakara bayan ta lashe Paris Saint Germain. Shin ko a kakar wasa ta bana Bayern Munich zata maimaita abin da tayi a kakar wasan data gabata?