By Abbas Yakubu Yaura
Hankula sun tashi a al’ummar yankin Ase-Omuku dake karamar hukumar Ndokwa ta Gabas a jihar Delta bisa wani shiri da wata kungiya da ba a bayyana sunanta ba ta shirya domin mamaye ta tare da cafke wasu ‘yan asalin kasar bisa zargin karya.
Da yake tsokaci a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a garin Warri a ranar Larabar data gabata, wani jigo a yankin, Cif Okwudili Obi, ya ce an shirya shirin girka ’yan bangar al’umma ne, wadanda suka ki bin tsarin zaman lafiya na gwamnatin jihar Delta.
Sanarwar ta tuno da yadda ‘yan sanda suka mamaye al’ummar tare da kama Obi, kasancewarsa mai sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin iyalan Ogbue da Onyeonwu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Rikicin da ya faru a tsakanin iyalan Ogbue da Onyeonwu ya faro ne a lokacin da aka kashe Francis Obi, a ranar 19 ga watan Nuwamba na shekarar 2013 a gaban ‘yan sanda, wadanda suka zo tare da marigayin domin su binciki lamarin kone-kone da wata kungiya da ake zargin Onyeanwu ne ta ‘yan uwa,” in ji sanarwar.
Yayin data kuma bayyana cewa daga karshe gwamnatin jihar ta kawo karshen rikicin, sanarwar ta bukaci sufeto-janar na ‘yan sanda da kwamishinan ‘yan sandan jihar da su ja kunnen jami’ansu da mazajensu kan tsoma baki cikin harkokin cikin gida na al’ummar Ase-Omuku.
Sanarwar ta kara da cewa, “Sufeto-Janar na ‘yan sanda da kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta ya kamata su gargadi jami’ansu da mazajensu da kada su kutsa cikin al’ummarmu domin kamo ’yan asalin jihar da ba su ji ba ba su gani ba, kan lamarin da gwamnatin Jihar Delta ta warware cikin lumana.
‘Yan sanda su kasance marasa son zuciya, rashin daidaito da bin doka a kowane lokaci. Muna adawa da duk wani yunkuri ko makirci na kara mamaye al’ummar Ase-Omuku domin kama mutanenmu bisa zargin karya’’.
Sannan ta bukaci CP da ya hana duk wani hari da kama shi ba bisa ka’ida ba a Ase-Omuku saboda hakan na iya haifar da rikicin kabilanci a cikin al’umma.