By Abbas Yakubu Yaura
Al’ummar Chamba mazauna Bisaula da ke karamar hukumar Kurmi a jihar Taraba a ranar Larabar da ta gabata sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta kafa kwamitin bincike kan rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kabilar Ichen da ‘yan Chamba a bisaula.
Mai-Angwa, Chamba-Bisaula, Bala Kukwa ne ya yi wannan kiran a cikin wata takardar daya aikewa manema labarai da ya sanyawa hannu a Jalingo.
A cewarsa, irin wannan hukumar za ta bankado abubuwan da suka haddasa tashe-tashen hankula a nesa da kuma na gaggawa domin samar da hanyar da za a maido da zaman lafiya a yankin.
Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya, Jiha da Kananan Hukumomin kasar da su gaggauta shiga tsakani ta hanyar tura karin jami’an tsaro a yankunan da ake fama da rikici kamar Gateri, Bisaula, Agabi da Sunkuru.
Kukwa ya kara da cewa, irin wannan matakin, da zarar shugaban karamar hukumar ya kai ziyara ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da kayayyakin agaji ga ‘yan gudun hijirar, ko kadan ba zai taimaka ba wajen kwantar da hankula.
Ya ce, “Mu al’ummar Chamba da ke Bisaula, muna kira ga gwamnatin jihar da ta kafa kwamitin bincike don gano musabbabin rikicin cikin gaggawa tare da ba da shawarar daukar matakan dakile sake afkuwar lamarin.
“Muna kuma rokon da a tura karin jami’an tsaro zuwa ga al’ummomin da ke fama da rikici don ceton rayuka da dukiyoyin mutanenmu.
“Ya kamata jami’an tsaro su saki ba tare da wani sharadi ba, an kamasu tare da tsare dukkan matasanmu bisa zalunci da rashin adalci da ‘yan kabilar Ichen suka kai.”
Kukwa ya nuna damuwarsa kan lamarin da shugaban kungiyar al’adu da ci gaban Ichen Dakta Ahmed Bibinu ya yi a kwanan baya kan lamarin, inda ya yi zargin cewa mutanen Dakka-Chamba mazauna Bisaula ne kawai.
“A cewar Bibinu, kabilar Chamba ta yi hijira zuwa Bisaula ‘a cikin shekaru 1930 ko suka koma wajen’. Idan kuwa haka ne, to yaya game da mutanen Ichen da suka yi hijira zuwa Bisaula kawai bayan shekaru 1961?
“Shugaban ICADA zai yi kyau ya samar da hujjojin da’awarsa da ikirarinsa,” in ji shi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa rikicin da ya barke a Bisaula a ranar 31 ga watan Disambar shekarar data ta 2021, tsakanin mutanen Ichen da Dakka-Chamba, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 8 daga bangarorin biyu, tare da lalata dubban mutane da dukiyoyi na miliyoyin Naira.