Rundunar Sojin Najeriya a ranar Alhamis ta bayyana cewa wasu batagari da suka yi niyyar shirin kawo cikas wajen gudanar da bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai da karun soji sun samu nasarar cafke su a ranar 1 ga watan Oktoba.
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Musa Danmadami, wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun taru a tsaunin Karshi da kewaye a cikin babban birnin tarayya, kafin shirin su ya ci tura.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘PDP Ba Zata Iya Dakatar Da Sata Ba’, Martanin Lai Mohammed Kan Kudin Da Mambobin NWC Suka Mayar
Danmadami ya ce sojojin sun kai farmaki kan tudu da kauyukan ne biyo bayan rahoton sirri da suka samu na shirin kawo cikas a bikin, inda ya ce an kama mutane 64 da ake zargi. Ya kuma kara da cewa mafi yawan wadanda ake zargin matasa ne sanye da bakaken kaya kuma suna dauke da bindigogi tara na gida.
Babban jami’in sojan ya ce sojojin sun kuma kai samame kan wata maboyar masu safarar miyagun kwayoyi ta hanyar Koroduma-Asokoro Guzape a karamar hukumar Abuja a ranar 25 ga watan Satumba inda suka kama wasu mutane biyar da ake zargi da sayar da miyagun kwayoyi.
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin dauke da jakunkuna 11 na abubuwan da ake zargin na tabar wiwi ta sata ce.
Ya kara da cewa, “A wani labarin kuma, an kama wasu mutane 33 da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne a wani wurin hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Gwagwalada. Dukkan wadanda ake zargin an mika su ga rundunar ‘yan sandan Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja domin daukar mataki.”
Da yake magana a kan sakin sauran mutane 23 da harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su, Danmadami ya ce an tabbatar da sakin wadanda abin ya shafa wanda kwamitin shugaban kasa ya aiwatar, yana mai cewa za a bayyana cikakken bayanin sakin wadanda aka kama.
A wani labarin kuma, Sama da Mutane 30 Sun Nutse A Ruwa, Bayan Sun Gujewa Harin Ƴan Bindiga
Akalla Mutane 30 da suka tsere daga harin da aka kai a yankin Birnin Waje da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara sun rasa rayukansu bayan da kwalekwalen da suka hau suka kife a daren Laraba.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa wasu kwale-kwale guda biyu makil da yawancinsu mata da kananan yara sun kife ne a lokacin da suke kokarin tsallakawa kogi don gujewa harin da wasu mutane dauke da makamai suka kai wa al’ummarsu.