Wasu ‘yan bindiga sun harbe shugaban wani ƙaramin gari tare da wasu mutum 17 a arewacin Mexico kamar yadda mahukunta kasar suka bayyana.
BBC ta ruwaito cewa, Yan sanda sunce ‘yan bindigar sun dira babban ɗaki’ taron garin Miguel Totolapan da misalin ƙarfe 7 na yamma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Batagari Sun Yi Shirin Kawo Cikas Don Ruguza Bikin Ranar Samun ‘Yancin Kai – Rundunar Soji
Tuni dai gwamnatin kasar ta Mexico ta yi Allah wadai da harin tare da neman gudanar da bincike domin hukunta masu hannu a lamarin.
Majiyar Jaridar Dimokiradiyya ta rawaito cewa, ‘yan sanda , da wazu Ma’aikata na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su.
A WNAI LABARIN KUMA:’PDP Ba Zata Iya Dakatar Da Sata Ba’, Martanin Lai Mohammed Kan Kudin Da Mambobin NWC Suka Mayar
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce ba zai taba yiwuwa jam’iyyar adawa ta PDP ta sauya sheka daga wawure dukiyar al’umma ba idan har ta samu damar mulki akasar nan.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a birnin Arusha na kasar Tanzaniya