By Abbas Yakubu Yaura
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a ranar Laraba da yamma a karamar hukumar Isuikwuato ta jihar Abia, sun yi awon gaba da fasinjoji a cikin wata motar safa tare da kai su cikin daji.
Basaraken al’ummar Umuanya da ke Uturu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Laraba, ‘yan kilomita kadan da jami’ar jihar Abia, Uturu, ya kara da cewa har yanzu ba a san makomar wadanda abin ya shafa ba.
Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa ‘yan bindigar da ake zargin dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da fasinjojin dake kan hanyar zuwa Akara a Isuikwuato daga tashar mota daura da jami’ar jihar Abia, Uturu.
Har ya zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, har yanzu ba a tantance wadanda lamarin ya shafa ba.
Duk kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Geoffrey Obonna, ya ci tura, domin ba ya karbar kiran da akayi masa.