Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi ne ke tafiyar da gwamnatinsa a matsayinsa na jagoran kasar.
Ndume ya yi wannan ikirarin ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Television’s Politics a jiya Juma’a.
Karanta nanNijeriya Da Jamus Sun Saka Hannu Akan Yarjejeniyar Samar Da Wutar Lantarki A Nijeriya
A cewarsa, Buhari ya taka rawar gani wajen sa ido, sabanin shugaba mai ci Bola Tinubu.
Mai tsawatarwa a Majalisar Dattawan ya ci gaba da cewa wasu kleptocrats suna cikin gwamnatin da ta gabata.
Yanzu shugaba Tinubu ne ke da iko,shine yake karbar ragamar mulki, sabanin tsohon Shugaban kasarmu, cewar Ndume
A nan ne matsalar take kuma shi (Buhari) ya san haka. Kuskuren da shugaba Buhari yayi kenan. Ya ƙare yana ikirari kwanakin nan cewa yana da ƙarin munafukai a cikin gwamnatinsa waɗanda mutane ne da ke da sha’awar son zuciya.
A halin da ake ciki, Ndume ya kuma kare salon yakin neman zaben shugaba Tinubu a zauren majalisar dokokin kasar a lokacin gabatar da kasafin kudin 2024.
A lokacin da Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin kudin a farkon makon, ‘yan majalisar sun tashi tsaye a matsayin alamar girmamawa, sai dai an ji kungiyar ta kunna wakar yakin neman zaben Tinubu tun lokacin yana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Yayin da ‘yan majalisar ke shan suka, Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu, yana ganin babu laifi a cikin matakin.
A wani labarin kumaBa Zamu Aminta Da Shigar Banza A Cocinmu Ba-Fasto Adeboye
Ya kara da cewa a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ‘yan majalisa ma sun yi ta karanta ‘sai baba’.
Ba laifi ba ne. Gaskiya ba wani abu bane babba. A kasar nan, muna ɗaukar abubuwa marasa mahimmanci. Lokacin da Shugaban kasa ya shiga, akwai lokacin da wasu membobin ke amfani da wannan yanayin har su kalubalanci shugaban kai tsaye.
Lokacin da Buhari ya shigo majalisa, an yi irin wannan abu ‘Sai Baba’ (an rera waka),don haka me zai sa lamarin Tinubu ya zama babba Yace.