By Abbas Yakubu Yaura
A safiyar ranar Asabar ne mayakan ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da Mista Reginald Ejiogu, babban limamin Ala Owerri, a karamar hukumar Owerri.
Jaridar Vanguard ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a titin Church Christ dake kan titin Ihugba a garin dake Owerri.
Sannan an ce an yi garkuwa da shi ne tare da wani shugaban kauyen Umunwagbara a karamar hukumar ta Owerri.
Sai dai aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Imo, PPRO, Micheal Abattam, yace a ba shi lokaci domin tabbatar da labarin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa tashin hankali ya dabaibaye majalisar karamar hukumar Owerri yayin da mazauna kauyen ke shirin sanin matakin da za a dauka na gaba.