Wasu ‘yan kasuwa biyu da jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA suka kama a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe, NAIA, Abuja bisa laifin hadiye hodar iblis dukkansu sun amayo da haramtattun kwayoyin guda 193 bayan kwanaki uku ana tsare dasu.
SOLACEBASE ta rawaito cewa masu safarar: Onoh Ebere mai shekaru 49 da Christian Ifeanyi Ogbuji mai shekaru 47, an kama su a filin jirgin saman Abuja a ranar Laraba 10 ga watan Mayu bayan da suka taso daga Uganda ta hanyar Addis Ababa, a cikin jirgin Ethiopian Airlines ET 951.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cikakkun Jerin Sunayen Ƙasashe Masu Yawan Jama’a da Matsayin Su a Duniya
Duk da cewa dukkan wadanda ake zargin suna da sana’o’in da suke gudanarwa a Najeriya, babban abin da suke samu shi ne safarar miyagun kwayoyi.
Dukkansu sun tafi Uganda ne daga nan suka wuce birnin Addis Ababa na kasar Habasha inda suka debi kayan kafin su koma Abuja da Legas a matsayin zangon karshe.
Wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar NDLEA Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi, ta ce bayan kwanaki a dakin da ake yin aman haramtattun kwayoyi, Ebere Onoh ya amayo da jimillar dauri 100 masu nauyin kilogiram 2.137 yayin da Christian Ifeanyi Ogbuji ya amayo da dauri 93 da ya boye a cikinsa mai nauyin kilogiram 1.986.
A halin da ake ciki kuma, jami’an hukumar NDLEA sun kai samame kan wasu mashahuran wuraren magunguna guda biyu, Zaro bunk a titin Bama, Sabongari da kuma filin wasa na Sani Abacha, duk a cikin birnin Kano, inda aka cafke mutane 160 da ake zargi da mu’amulla da haramtattun kayayyaki iri-iri.
Haka kuma an kama wasu mutane biyu Abubakar Sallau mai shekaru 55 da Nazifi Abdullahi mai shekaru 25 a ranar Asabar 13 ga watan Mayu a kan hanyar Kano zuwa Maiduguri tare da kwayoyin Tramadol 200mg guda 5,000, yayin da aka kama duka allunan tramadol 65,200 da kuma exol-5,daga hannun yan biyun Adamu Nagati mai shekaru 30 da Ali Nasiru mai shekaru 35.
A wani labarin kuma, Fasfo: An Gurfarnar da Jami’ai 80 Gaban Shari’a, An Kori Wasu 8 – NIS
Akalla jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) guda 80 ne aka gurfanar da su gaban kuliya bisa samun su da laifin karban kudade ba bisa ka’ida ba na fitar da sabbin fasfo da sabunta tsofaffi.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar SPRO, Mista Tony Akuneme, wanda ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Abuja, ya kuma nuna cewa an kori wasu jami’ai 8 daga bakin aiki wadanda suka aikata laifi iri daya a cikin shekara daya.