Yanzu haka dai wata kididdiga ta bayyana kasashen duniya da ke da mafi yawan al’umma wadanda aka ba su matsayi.
Kididdigar da aka fitar ta baya-bayan nan ta sanya Indiya a matsayi ta ɗaya a cikin ƙasashen da suka fi yawan jama’a a duniya, sai China, Amurka, Indonesiya da Pakistan da ke biye da su,kamar yadda Daily Post ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fasfo: An Gurfarnar da Jami’ai 80 Gaban Shari’a, An Kori Wasu 8 – NIS
Najeriya ce kasa mafi yawan al’ummar bakar fata a duniya kuma tana a matsayi na 6 a duniya.
Kasashe mafi ƙanƙantar yawan jama’a sun haɗa da Iceland mai yawan mutane 374,788, Seychelles – 107,660 217, Monaco – 36,297, 227, Tuvalu – 11,396, 234 da Vatican – 518
Cikakken jerin sunayen kasashen gashi kamar haka:
- 1. Indiya – 1,426,409,584
- 2. China – 1,425,731,257
- 3. Amurka – 339,688,556
- 4. Indonesia – 277,148,717
- 5. Pakistan -239,693,115
- 6. Najeriya – 222,914,017
- 7. Brazil – 216,214,106
- 8. Bangladesh -172,659,039
- 9. Rasha – 144,528,119
- 10. Mexico – 128,297,060
- 12. Japan – 123,405,307
- 18. Turkiyya – 85,740,393
- 19. Jamus – 83,300,994
- 21. Ingila – 67,698,634
- 23. Faransa – 64,735,380
- 24. Afirka ta Kudu – 60,322,787
- 25. Italiya – 58,899,388
- 29. Koriya ta Kudu – 51,790,420
- 33. Argentina – 45,725,645
- 38. Kanada – 38,726,161
- 55. Ostireliya – 26,395,113
- 72. Netherlands – 17,609,287
- 87. Sweden – 10,601,484
- 96. Hadaddiyar Daular Larabawa Dubai UAE – 9,504,149
- 100. Ostiriya – 8,955,779
- 101. Switzerland – 8,787,128
- 114. Singapore – 6,008,362
- 115. Denmark – 5,906,142
- 119. Norway – 5,467,469
- 168. Luxemburg – 653,708
- 179. Iceland – 374,788
- 197. Seychelles – 107,660
- 217. Monaco – 36,297
- 227. Tuvalu – 11,396
- 234. Vatican – 518
A wani labarin kuma, Dalilin Da Yasa Bana Bugawa Manyan Kungiyoyin Turai Wasa — Okocha
Tsohon kyaftin din Super Eagles, Austin ‘Jay Jay’ Okocha, ya bayyana dalilin da ya sa baya buga wasa a manyan kungiyoyi Turai a lokacin da yake buga wasa.
A cewarsa, manyan kungiyoyin ba su ba shi kwangiloli masu tsoka ba.
Allah ka rabamu da duniya lafiya.