By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta cafke wasu matasa uku da ake zargi da yunkurin kisan kai don yin tsafi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce an kama wadanda ake zargin tare da hadin gwiwar matasan unguwa a karamar hukumar Sagbama.
Wadanda ake zargin dai sun hada da Emomotimi, Perebi da Eke, Wadanda ake zargin ‘yan shekaru 15 ne.
Sanarwar ta ce, sun kama wata mai suna Comfort mai shekaru 13 da haihuwa, ta bi su zuwa gidan Emomotimi da ke unguwar Sagbama, inda suka yanke mata yatsu tare da yayyafa jinin akan madubi domin yin tsafi.
“Sauran da suka yi taka-tsantsan sun lura da motsin wadanda ake zargin suna tayar da hankali a yankin.
“Daga baya an kama wadanda ake zargin kuma an kwato wasu abubuwa da ake zargin layu ne daga hannunsu. Wadanda ake zargin dai sun amince da aikata laifin.
“An ceto wanda lamarin ya rutsa da ita tare da garzayawa da ita zuwa asibiti domin kula da lafiyarta.An mika wadanda ake zargin zuwa sashin yaki da masu garkuwa da mutane domin gudanar da bincike mai zurfi.”
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bayelsa, CP Ben Okolo, ya yabawa matasan al’ummar bisa yadda suke taka-tsantsan kan lamarin.