Wata Ƙungiya mai zaman kanta ta buƙaci FG da ta sanya ilimin zaman lafiya a cikin darussan karatu a Najeriya
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Gidauniyar kare yara da matasa ta CYPF ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ilimin zaman lafiya a cikin jerin darussan ilimi na kasa da ake koyarwa a makarantu.
Ko’odinetan Kungiyar ta CYPF Kolawole Olatosimi ya yi wannan kiran a ranar Talata a Abuja gabanin gudanar da bikin ranar ilimi ta duniya da aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Janairu.
A cewarsa manufar ciyar da zaman lafiya da samar da ci gaba ta hanyar ilimi bai taba zama mara muhimmanci ba.
Ya kuma ƙara da cewa ya dace duk masu ruwa da tsaki su yi ƙoƙarin samar da wannan damar domin ilimin zaman lafiya ya iya isa ga dukkan ɗalibai a kowane mataki na ilimi a faɗin Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN:Igbo ne za su tantance shugabancin ku kan yadda kuke tafiyar da Nnamdi Kanu – Ejimakor ga Tinubu
Bugu da ƙari, yana da mahimmanci a inganta tsarin karatu wanda ke jaddada ba kawai ilmantarwa na ilimi ba har ma da haɓaka kaifin tunanin ɗaliban wanda hakan yana da matuƙar mahimmanci, da ma sauran mahimman basira don samun ingantaccen zaman lafiya.
Domin samar da dawwamammen zaman lafiya dole ne ba wai kawai mu saka hannun jari a fannin ilimi ba, face har ma mu tabbatar da cewa yana da inganci kuma ya dace da bukatun al’ummar mu,” in ji Olatosimi.
Olatosimi ya ce ilimi wani kayan aiki ne mai karfi na samar da duniya mai zaman lafiya domin yana rage rikici da tashin hankali ta hanyar inganta fahimta da juriya yayin fuskantar Jarabawa.
Ya bayyana cewa ilimi yana kuma baiwa daidaikun mutane kwarewa da ilimin da ake bukata don magance matsaloli da kuma samar da hanyoyin warware rikici cikin lumana.
A wani labarin kuma:Gwamnan Filato ya ayyana dokar ta ɓaci a wata ƙaramar hukuma
Gwamnan Filato ya ayyana dokar ta ɓaci a wata ƙaramar hukuma
Gwamna Caleb Mutfwang na Filato ya kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Mangu tare da fara aiki nan take.