Cibiyar Zaɓe ta Turai, dake ƙarƙashin ƙungiyar Ƙasashen Turai ta bayyana ƙudirin ta na inganta ƙwazon ƴan jarida a kawo rahoton zaɓe.
Jami’in Ƙungiyar Mr Hamza Fassi-Fihri ya bayyana haka a ranar Talata a Enugu a lokacin taron Kafafen Yaɗa Labaru gabanin zaɓen ranar 23 ga watan Fabrairu na shekarar 2022, zaɓe Jahar Enugu.
KARANTA WANNAN LABARIN: YANZU-YANZU: Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kafa Sabbin Makarantun Horas Da Aikin Lauya
Ƴan Jarida guda 30 da aka zaɓo a kafafen yaɗa labaru na jarida da rediyo da talabijin suka halarci taron ƙara ilmin wanda ya gudana a otal na Maxbe.
Fassa-Fihri a jawabin sa, yace taron horaswar nada manufar inganta kawo rahotannin zaɓe.
Yace “ilmi ya nuna cewa babu wata Dimokuraɗiyya idan babu Kafafen Yaɗa Labaru mai gashin kanta. Kuma babu kafafen yaɗa labaru ba tare da ƴan jarida ba. Wannan ne ya sanya dole ga ƙara ƙwazo domin horas da ƴan jarida, bada gudunmawa akan cigaban su da ilmin su.”
Ya kuma bayyana cewa horaswar na wani ɓangare na aikin gidauniyar na bayar da taimako na sanin makamar aiki ga Hukumomi na zaɓe a faɗin duniya.
Ya ƙara dacewa aikin nada manufar taimakawa Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da Hukumomin Zaɓe na Jahohi a Najeriya.
Comments 1