Herconomy Ƙungiya dake manufar tallafawa mata, tace ta tara Dala $600,000 domin tallafawa mata a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da suka fitar a Lafiya, Shugabar Ƙungiyar Ifedayo Durosinmi ta bayyana cewa ƙungiyar na bakin ƙoƙarin ta domin tabbatar dacewa an tallafawa mata domin su zamanto masu ƙarin daraja a cikin Al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Omicron: Gwamanatin Lagos zata hukunta duk wanda ya karya dokar kariyar cutar COVID-19
Tace “wannan shekarar Ƙungiyar Herconomy Cooperative Multipurpose Society, an bayyana a matsayin wanda ta ɗauki wani tafarki na tallafawa Al’umma musamman mata a Najeriya.
“Domin cimma muradun ta, ƙungiyar tuni ta fara tattara kuɗaɗe, kuma a halin yanzu sama da mata ɗari 500 sun samar da Dala $100,000 a cikin watanni shida.
Durosinmi-Etti ta ƙare dacewa, za’ayi amfani da waɗannan kuɗaɗe domin inganta kayayyakin su, da haɓɓaka kasuwa da wasu harkoki.