Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun cafke wata budurwa wadda ake zarginta da laifin shekawa wani saurayi ruwan shayi a jikinsa.
Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar manema labarai a Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Mummunar Guguwar Iska Ta Hallaka Mutane 7 A Italiya
Kiyawa yace, “lamarin ya faru ne a unguwar Rimin Auzunawa, inda Maryam Haruna ta kona wani saurayi Lawan Inuwa da tafashasshen ruwan Shayi.”
Ya kara da cewa “bayan sun sami korafin ne rundunar ta aike da jami’anta zuwa gurin inda suka dauki matashin tare da garzayawa dashi zuwa Asibiti domin ceto lafiyarsa.”
Budurwar mai suna Maryam Haruna da ake zargi da aikata laifin shekawa saurayin Lawan Inuwa ruwan zafi tare da kona shi,tace sun sami sabani dashi ne kuma tsautsayi yasa ta dauko ruwan shayi ta sheka masa a jikin sa.
Sai dai rundunar ‘yan sandan ta gargadi mutane dasu kaucewa daukar doka a hannu musanman domin gujewa fadawa tarkon dana sani.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayya zata Kafa Bankunan Matasa
Ministan Matasa da Cigaban Wasanni Sunday Dare, ya ce gwamnati na shirin samar da asusun zuba jari na matasa na kasa (NYIF) don ya zama Bankunan Matasa.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a taron karawa juna sani na ministoci karo na 51 da kungiyar sadarwar fadar shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa, Abuja.