Wata budurwa ƴar Najeriya ta nunawa duniya tagomashin da ta samu bayan ta kwashe kuɗin makarantarta ta fara kasuwanci da su.
Budurwar ta nuna ƙayataccen wajen da take aiki shekara uku bayan ta fara kasuwanci da kuɗin makarantar ta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Allah mai iko: Bidiyon wata ɗaliba mai lallurar makanta mai yin kitso ya ɗauki hankula sosai
Budurwar wacce ta kammala karatunta a jami’ar jihar Legas, ta bayyana yadda wata rana tana kwance a kan gadon ta yadda wata dabarar fara sana’ar abinci ta faɗo mata.
Ta bayyana cewa ba tayi wata-wata ba ta kwashe kuɗin da zata biya kuɗin makaranta da su ta fara sana’ar.
Ta bayyana kasuwancin da ta fara a matsayin wani babban ƙalubale wanda ya fi sauran dukkanin ƙalubalen da ta taɓa fuskanta a rayuwar ta.
Wasu daga wahalhalun da ta fuskanta wajen yin gurin kasuwancin nata sun haɗa da rashin kyawun hanya, matsalar ƴan daba da rashin tsaro.
Mutane da dam sun yaba mata kan jajircewar da ta nuna wacce ta kawo ta a matsayin da take a yanzu.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin mutane da Dimokuradiyya ta tattaro:
Oladunni_mike ya rubuta:
“Wai a ina kuke ganin irin wannan kuɗin ne? Kasuwanci a Najeriya bana rago bane. Ina taya ki murna CEO. Kin cancanci a yaba miki.”
@thefestusakande ta rubuta:
“Wannan ya ƙaramin ƙwarin guiwa sosai. Tabbas na yarda dake..Kasuwanci na da matuƙar wahala.”
3 years ago I laid on the student bed , unsure of what the future holds , an idea came to my head and immediately took my school fee to commence it
This day , 3years later , this is how far that has brought us
This project is the toughest I have ever had to do pic.twitter.com/AnalWT8Phd
— Techpreneur 👩💻💵 (@Ade_authority) January 17, 2023
Cristiano Ronaldo Ya Samu Wani Babban Matsayi a Wasan Da Za Suyi Da Kulob Ɗin Messi
A wani labarin na daban kuma, Cristiano Ronaldo zai jagoranci tawagar zakarun ƴanwasan Saudiyya a fafatawar da za suyi da Paris Saint Germain.
Shahararren ɗan wasan ƙwallon kafar nan wato Cristiano Ronaldo, zai jagoranci tawagar zakarun ƴan wasan Saudiyya a fafatawar da za suyi da kulob ɗin PSG, s wani wasan sada zumunta ranar Alhamis, 19 ga watan Janairun 2023.
Wasan shine zai kasance wasa na farko da Cristiano Ronaldo zai fara bugawa tun bayan da ya koma kulob ɗin Al-Nassr, a wata yarjejeniya wacce za ta sanya ya riƙa samun £175m duk shekara. Zai jagoranci tawagar su wacce ta ƙunshi ƴanwasa daga kuloblukan Al-Nassr da Al-Hilal.