Wata dattijuwa ‘yar shekara 81 da haihuwa a duniya, Allah ya nufa ta samu nasarar sauke al’qur’ani mai girma a Kano
Matar mai suna Hajiya Asma’u Jibrin wacce daliba ce a makarantar Hajiya Baraka Islamiyya Bachirawa Karamar Hukumar Ungogo, ta kasance guda daga cikin daliban makarantar 12 da suka yi saukar qur’ani a karshen makon nan.
KU KARANTA: Babu Batun Mu marawa Tinubu Ko Atiku Baya – SDP
A hirarta da manema labarai, Hajiya Asma’u ta bayyana kadan daga cikin abubuwan da suka taimaka mata wajen samun wannan nasara ta sauke al’qur’ani mai girma.
A cewar dattijuwar tun tana karama ta taso da shauki da san ta samu ilimi kasancewar mahaifinta malami ne, wannan yasa ta kwadaitu da sha’awar taga ta gaje shi.
Da yake sawa Daliban albarka Mai girma Magajin Malam, Hakimin Ungogo, Alh Abdulkadir Ahmad Chedi, wanda Mukaddashinsa Malam Lawan Malami Ungogo ya wakilta a wajen taron saukar, ya ja hankalin al’umma da su tashi da addu’o’i babu dare ba rana don ganin anyi zaben kasar nan an kammala shi lafiya.
Malami Ungogo yace zaben bana ba na kudi bane, dole ne al’umma su yi addu’a su kuma zabi cancanta idan baso suke su dauwama a cikin wahala ba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Daga bisani basaraken ya shawarci daliban makarantar da su cigaba da karatun qur’anin da sauran litattafai da kuma kokarin kamanta aiki da hukunce hukuncensu.
A wani labarin kuma: Yan sanda sun kama wani likitan jabu bayan shafe watanni 10 yana aiki
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani likitan jabu wanda har yanzu ba’a tantance ba wanda ke aiki tun watan Janairun 2022.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin, wanda ya bayyana hakan a wani sakon Twitter a ranar Asabar, ya ce wanda ake zargin yayi karyar takardar shaidar likita da sunansa.
A cewarsa, wasu mazauna jihar ne suka hango wanda ake zargin kuma suka mikawa rundunar bayanan.