Wata babbar kotun tarayya da ke karkashin Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa da ke zamanta a Kano, ta dage cewa dole ne Alhaji Abdusalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, wanda shi ne dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, ya amsa zargin damfarar dala miliyan 1.3 da ake tuhumarsa da shi.
Yayin da aka ci gaba da sauraren karar a yau Alhamis, Mai Shari’a Yunusa ya tsaya kan cewa matsayin tsarin mulki da doka shi ne AA Zaura da ake zargi da damfarar wani wanda ba dan Najeriya ba har dala miliyan 1.3 dole ne a gurfanar da shi gaban kotu kafin a saurari wani batu.
KARANTA ANAN: Bamu Da Hannu A Soke Takarar Gwamnan PDP A Zamfara – APC
Lauyan AA Zaura, Barista Ibrahim Waru, ya ce a matakin farko kotun ba ta da hurumin sauraren karar saboda wanda yake karewa ya daukaka kara kan hukuncin da wata kotun daukaka kara ta tarayya ita ma da ke Kano ta yanke.
Sai dai alkalin kotun ya ce ya zama wajibi kotunsa ta saurari karar saboda ba su samu sanarwar daukaka kara ba, don haka dole ne a gabatar da AA Zaura a kotun.
Don haka a matsayin Kotu, Lauyan Hukumar EFCC, Barista AI Aroghn, ya ce za su tabbatar sun gabatar da Zaura a gaban kotu, ciki har da kama shi idan ya ki zuwa kotu.
Mai shari’a Yunusa ya dage sauraron karar don gurfanar da AA Zaura da sauraron karar zuwa ranar 5 ga Disamba 2022.
Idan dai za a iya tunawa dai Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a zaman kotun da ta gabata ta bayyana cewa, Zaura da ke shari’ar da ake yi wa shari’a a kan wasu makudan kudade dala miliyan 1.30 ba a san daga inda ya samo su ba, kuma ya kasa bayanin yadda ya same su.
A wani labarin kuma: Jihar Nasarawa Ta Sami Sabon Kwamishinan Yan sanda
An tura sabon kwamishinan ‘yan sanda (CP), Maiyaki Muhammed-Baba, zuwa jihar Nasarawa.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Nansel Rahman, ya fitar, ya ce sabon Kwamiahinan ya karbi ragamar rugudanar ne daga hannun Mista Adesina Soyemi wanda a kwanan nan aka kara masa mukamin mataimakin sufeto Janar (AIG) na ‘yan sanda.