Kungiyar masu cutar Numoniya ta Nijeirya ta rabawa fiye da 200 da atamfofi da wadansu kayayyakin ga zawarawa da suka rasa mazajensu sojoji da wadanda kuma mazajensu suka yi ritaya daga aikin soja.
Fatima Idris Danjuma, shugabar kungiyar ta kasa ta ce sun yi haka din ne a wani mataki na rage radadin da suke fuskanta a daidai lokacin bukin tunawa da sojojin Nijeriya ta 2021 da ya gudana a Bauchi.
A cewarta, za su ci gaba da yin hakan a duk fadin Nijeriya ciki harda birnin tarayya Abuja. Ta nuna yadda iyalin sojojin suke cikin wani irin kangi na wahala, idan ta yi kira ga al’umma da su rika tallafa musu domin rage musu wannan radadin.