Wata ma’aikaciyar banki mai shekaru 32 ta hallaka kan ta
Rashin kwanciyar hankali ya mamaye daya daga cikin bankuna na farko a yankin Ikorodu da ke jihar Legas, biyo bayan gano gawar daya daga cikin ma’aikatan da ba ta da rai, a kasan bandakin bankin.
Marigayiyar mai suna Amarachi Ugochukwu, an ce ta kashe kanta.
An samu takardar kashe kanta da maganin kwari da ake zargin ta sha a kasan bandakin.
KARANTA WANNAN LABARIN:A yau Kotun koli za ta raba gardama a jihohin Kano, Plateau, Legas, da wasu 4
Marigayiya Amarachi, ma’aikaciyar Talla ce, kamar yadda abokan aikinta suka bayyana, ta bar teburinta da misalin tsakar rana, ranar 8 ga Janairu, 2024, don samun sauki.
Rashin dawowar ta ne yasa aka lura da ita,bayan wayarta da ta ajiye akan tebir bata tafi da’ita ba
Saboda sha’awar, an ce wasu abokan aikinta sun neme ta a cikin harabar.
Daya daga cikinsu da ya je nemanta a bandaki, an ce ya tarar a kulle daga ciki. Tsanani ne ya sanya lokacin da aka buga k’ofa baya yawan shiru da ya yi yawa daga ciki.
Da k’ofar aka bud’e aka same ta a k’asa ba motsi.
Littafin ta na 2024 wanda a ciki ta rubuta bayanin kashe kansa ya karanta: “Babu wani abu da ke aiki a rayuwata. Kwakwalwa ta toshe. Tattalin Arziki yana ƙara yin wahala. Shawarwarina ba daidai ba ne. Hankalina ya tashi. Nan gaba ba ta da alama ko kaɗan, ina ganin matsananciyar wahala, kuma ba zan iya jure zafin ba. Yi hakuri Mama, hakuri Baba.
Ta kuma nemi afuwar wasu mutane biyar, inda ta ambaci sunayensu sannan ta karasa maganar da “Ya Ubangiji ka ji tausayina”.
Abokan aikinta sun ce wani likita da aka gayyata, ya tabbatar da cewa ta rasu.
Tawagar ‘yan sanda reshen Ikorodu da suka ziyarci wurin da lamarin ya faru bayan samun labarin sun kwashe gawar zuwa babban asibitin Ikorodu domin a duba gawar.
Majiyoyin ‘yan sanda sun yi nuni da cewa an tuntubi iyalan marigayin.
A wani labarin kuma:Falana ya fitar da shawara ga Tinubu kan abinda ya kamata ya yi kan matsalar tsaro
Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya kira taro da rundunar ‘yan sandan Najeriya domin tsara hanyoyin dakile matsalar rashin tsaro a kasar.
Falana ya yi wannan kiran ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Television ya yi dashi a ranar Alhamis.