By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wata matar aure ‘yar shekara 30 mai suna Cynthia Olukiowu da laifin dabawa wani dan wan mijinta Habeeb Aremu mai shekaru 18 wuka wanda ta kashe shi har lahira.
Wanda ake zargin tana zaune a wuri mai lamba 2, kan titin Apogidonoyo, Jafa Agbado, a karamar hukumar Ifo ta jihar, an kama ta ne a ranar Asabar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP, Abimbola Oyeyemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an kama Olukiowu ne biyo bayan kiran da ‘yan sandan da ke hedikwatar sashin Agbado suka samu.
Ya bayyana cewa an shaida wa ’yan sanda cewa matar kawunsa ta daba wa wani yaro wuka a wuya bayan marigayin ya karya madubi.
Oyeyemi ya ce, “An bayyana cewa madubin da ake amfani da shi a gidan ya karye kuma ana zargin marigayin da fasa shi.
“Zarge-zargen ne ya haifar da rashin jituwa tsakanin marigayin da matar kawun nasa, inda daga baya wanda ake zargin ta dauki wukar dakin dafa abinci ta yi amfani da ita wajen daba wa marigayin wuka a wuyansa.
“Bayan wannan kiran na bakin cikin, DPO, reshen Agbado, CSP Kehinde Kuranga, ya yi gaggawar kai mutanensa wurin da lamarin ya faru, inda ba tare da bata lokaci ba aka cafke wanda ake zargin, sannan aka garzaya da wanda ake zargin yana cikin jini.
“Abin takaici Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsa kuma an ajiye gawar tasa a dakin ajiye gawa na babban asibitin Ifo domin a duba lafiyarsa.”
PPRO ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin cikin gaggawa zuwa sashin binciken laifuka da leken asiri na jihar domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.