Wata matashiya ‘yar shekara 38 mai fafutukar ganin ci gaban matasa, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta zama mace ta farko da ta bayyana sha’awarta ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 mai zuwa. Okunnu-Lamidi, a ranar Litinin, ta bayyana sha’awarta na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin Shugabancin Najeriya.
Okunnu-Lamidi diyar Babban Lauya Lateef Femi Okunnu (SAN) ce, tsohon kwamishinan ayyuka da gidaje na tarayya, wanda shi ne shugaban kungiyar Isale-Eko Descendants Union kuma dattijon jiharsa, yayin da mahaifiyarta, Arinola Omololu, ta kasance hamshakiyar ‘yar kasuwa ce, kafatanin Zuri’ar su ta Ago-. Owu .
Da take magana a wani taron manema labarai da aka gudanar a filin shakatawa na Freedom da ke Legas, Okunnu-Lamidi, wata kwararriya ce, mai fafutukar ganin an gudanar da ayyukan Ci gaba ga na zamantakewar al’umma, wacce ta zama Kuma sananniya a kafafen yada labarai na Kasa, da kuma yin tallata tallace-tallace, ta bayyana cewa dalilinta na neman kujerar shugaban kasa ya samo asali ne daga sha’awarta na yin takara. Domin ganin Najeriya ta yi aiki ga al’ummar kasar daban-daban.
Comments 1