Lamarin ya auku ne lokacin da direban ke kokarin kaucewa wata mota dauke da fetir inda yayi kokarin wuce ta.
Fasinjojin motar Hudu ne suka jikkata ciki har da direban yayin da wasu suka tsallake rijiya da baya Wanda hakan ya haifar da cinkoso kan gadar Afa isolo dake legas.
Shedun gani da ido ya shaidawa majiyar mu cewa lamarin ya auku ne a safiyar talata dai dai lokacin da ‘Yan makaranta da ma’aikta da ‘Yan kasuwa suke kokarin fita daga gidajen su.
Dalilin Gobarar motar shine salansar motar ce ta kwashi fetir da ya zuba a hanyar saboda mai ya malala kan titin sai ta ringa digar da mai Wanda hakan yasa ta kama inji shi.
Yace abun na faruwa aka garzaya da su asibiti ba ba ta lokaci.
Motar man tun 5:50 na yamma ta mutu inda jami’an bada hannu da na hukumar kashe gobara suka gefantar da motar.