Wata Sabuwa: Ƙungiyar Ƙwadago ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnati
Wata gaggarumar tarzomar yajin aiki ta kunno kai a jihar Kwara yayin da kungiyoyin kwadago suka bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar kan rashin biyan bukatunta.
Bukatun, a cewar Murtala Saheed Olayinka, Tunde Joseph da Saliu Suleiman, shugabanin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC a jihar, sun hada da rashin aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 35 biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zulum ya rattaba hannu kan kasafin kudin jihar Borno na Biliyan 358.7
A wani taron manema labarai da suka gudanar a Ilorin, kungiyar kwadagon ta kuma koka kan kin amincewa da gwamnatin jihar na ƙin aiwatar da kashi 40 cikin 100 na alawus alawus kamar yadda gwamnatin tarayya ta amince.
Sauran bukatu sun hada da biyan ’yan fansho da aka yi musu gyara tun bayan amincewa da sabon mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta yi a shekarar 2019 da kuma rashin biyan ma’aikatan kananan hukumomin basussukan da suke bi.
Ƙungiyar ta kuma yi Allah wadai da rashin isassun kudade na manyan makarantun jihar, da rashin son daukar ma’aikatan Otal din Kwara ba tare da wani sharadi ba da kuma rashin sanya ma’aikatan kamfanin ruwa da aka sake tura su cikin babban ma’aikatan jihar ta Kwara.
Kungiyar kwadagon ta ce dole ne ta bayar da wa’adin ganin yadda gwamnatin jihar ta ki amincewa da bukatar ma’aikatan gwamnatin jihar, wanda hakan ya sanya fargabar zaman lafiya da kwanciyar hankali a masana’antu.
A wani labarin kuma:Rahotan BBC: DSTV Zai cire tashar da Fasto TB Joshua ya kafa
DSTV ta sanar da masu kallo aniyar ta na dakatar da watsa shirye-shiryen gidan talabijin na addini, mai suna Emmanuel TV.
Marigayi wanda ya kafa Cocin Synagogue Church of All Nations, SCOAN, T.B Joshua ne ya kafa Emmanuel TV.
Wannan ci gaban ya biyo bayan wani fim mai cike da cece-kuce a kan malamin da BBC ya fitar.