Wata Sabuwa: Sama da Ƴan Takara 120 sun nemi APC ta dawo Masu da Kuɗin Tsayawa Takara
Wasu ‘yan takara da suka fafata a Babban taron zaɓen Shuwagabannin jam’iyyar APC mai mulki a ranar 26 ga watan Maris, sun sha alwashin gurfanar da shugabannin jam’iyyar a gaban ƙuliya bisa rashin mayar da kudaden da suka biya na fom din nuna sha’awa da tsayawa takara.
Wannan ci gaban dai na zuwa ne watanni hudu bayan an nemi su janye akan mukamin shugaban jam’iyyar na kasa mai ci Sanata Abdullahi Adamu da sauran mambobin kwamitin ayyuka na kasa.
Wasu ’yan siyasa da abin ya shafa da suka yi magana a wata tattaunawa daban-daban, sun bayyana damuwarsu da cewa sun yi bincike tare da ganowa ba komai bane zai hana su zama Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa.
Ya danganta da nau’in fom na neman tsayawa takara, mutane 126 da suka tsaya takara a mukamai daban-daban sun yi tarin kuɗi tsakanin Naira miliyan 20 zuwa miliyan 2.5.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rashin tsaro: Ƴan sanda sun Cafke Ɗan Ta’addan dake Shigar Mata
A karshen zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar, APC ta tara sama da Naira miliyan 700 tare da ƙarin Naira biliyan 3 da aka samu tsakanin masu ruwa da tsaki da ‘yan jam’iyyar gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa.
An kuma yi korafin cewa duk da dimbin kudaden da shugabannin jam’iyyar suka samu a tsakanin watan Maris zuwa Agusta, ma’aikatan wucin gadi da ma’aikata da kuma ‘yan jam’iyyar da abin ya shafa da suka yi aikin zaɓen, ba a biya su alawus-alawus ba.
*An Nemi Ƴan Takara su janye a babban taron kasa*
‘Yan takarar da abin ya shafa da suka janye wa Adamu a matsayin shugaban Jam’iyyar APC na kasa sun hada da Sanata Umar Al-Makura, Salihu Mustapha, Muhammed Sani Musa, Abdulaziz Yari Abubakar, Sanata George Akume da Mohammed Etsu.
Wadanda suka janye a ɓangaren Mataimakin Shugaban Kasa (Arewa) da suka janye saboda amincewar Sanata Abubakar Kyari, sun hada da Yakubu Dogara, Faruq Aliyu, Sunny Sylvester Monidefe, Sanata Ken Nnamani, Malam Isa Yuguda da Emmanuel Joseph.
A muƙamin sakataren jam’iyar na ƙasa, mutane uku da suka tsaya takara da suka hada da tsohon Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu; Oyedele Ifeoluwa da Farfesa Olaiya Olaitan sun sadaukar domin takarar Sanata Iyiola Omisore.
A bangaren mataimakin shugaban kasa (South-South), Yekini Nabena da Worgu Chambers an nemi su barwa Victor Giadom.
Baya ga ’yan takarar da aka ambata, akwai wasu ’yan siyasa 113 da su ma ba a biya su kudadensu ba.
Daya daga cikin ‘yan takarar da abin ya shafa, wanda ya zanta da wakilinmu, ya sha alwashin mayar da fom din tsayawa takara kafin Adamu yabar mukaminsa.
*Adamu ‘da gangan’ ya jinkirta maida kudin su*
Ya ce, “Mun san nawa aka samu a taron da ma zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC. To mene ne matsalar? Mu ’yan jam’iyya ma muna da yakini cewa an samu kuɗi, amma anƙi maido mana.