Hukumar lafiya ta duniya WHO ta nemi tallafin dala miliyan 675, kwatankwacin kusan naira biliyan 245, domin yaki da cutar ‘Coronavirus’ ta hanyar zuba hannun jari a kasashen da suke cikin hadarin kamuwa da cutar.
Shugaban WHO Tedros Ahanom Ghebreyesus ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na duniya da aka gudanar a Geneva babban birnin kasar Switzerland.
Ya ce dala milyan 60 na kudin zai zama na amfanin WHO, yayin da ragowar kudaden kuma za a taimaka wa kasashe don kare su daga coronavirus.
A cewarsa, WHO za ta aike takunkumin kariya 500,000 da abin shakar iska 40,000 zuwa ga kasashe 24.
Tedros ya kuma yaba da tallafin dala miliyan 100 daga gidauniyar ‘Bill and Melinda Gates’ domin yin gwajin cutar da kula da masu ita da kuma bincike kan maganinta.