William Saliba ya kara kwantiragin cigaba da zama a Arsenal tsawon,shekaru biyar wanda zai barshi a kungiyar har zuwa shekarar 2028
Saliba wanda yazo Arsenal a shekarar 2019 daga Saint Etienne akan yuro miliyan 27,ya nuna matukar kwarewa wajen tsaron bayan Arsenal a tsawon shekarun daya kwashe a Emirates Stadium
Saliba ya bi sahun sauran abokan wasansa na Arsenal wajen kara kwantiragi a Arsenal,da suka hada da Bukayo Saka,Aron Ramsdale da kuma Gabriel Martinelli
Yayinda dake kokarin dauko sabbin yan wasa da suka hada da kyaftin din West Ham United dan asalin kasar Ingila da Declan Rice da kuma Jurien Timber wanda ke wasa a kungiyar Ajax
Arsenal na neman kara karfafa yan wasanta domin tunkarar kakar badi don gujewa abin da ya faru da ita a bana inda bayan shafe watanni takwas akan teburin Firimiya
KARANTA NANTinubu Ya Jinjinawa Shugaban Kasar Senegal Kan Kin Neman Kujerar Sa A Wa’adi Na Uku
Manchester City ta lashe Kofin bayan yin nasarar a wasanni goma a Jere,abinda mafi yawancin masana harkar kwallon kafa suka kira da abu mai kamar wuya
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya matukar yaba ma Saliba wanda ya kira jajirttaccen dan wasa kuma mai hazaka wanda baya wasa da aikinsa na tsaron baya
Hakan yasa Kocin yayi duk mai yiwuwa wajen ganin dan kasar Faransar mai shekaru 22 ya kara sabon kwantiragi na shekaru biyar
A WANI LABARIN KUMA
Bukatar Man Fetur Ta Ragu Da Kashi 28 Cikin 100,Tun Bayan Cire Tallafin Mai-NNPC
Hukumar kula da man fetur ta Najeriya sun bayyana cewar bukatar man fetur a Najeriya ta matukar raguwa da kashi 28 cikin 100 tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnati tayi
Sabuwar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin mai bayan karbar mulki daga tsohon shugaba Muhammadu Buhari,abinda tun lokacin yakin neman zabe ya kuduri aniyar yu