- Ya bayar da ƙodarsa domin a sanyawa mahaifiyarsa da take fama da ciwon ƙoda.
- Bayan da aka cire masa ƙodar, sai Allah yayi masa rasuwa ita kuma mahaifiyar ta rayu.
- Labarin ya ja hankalin ma’abota amfani da shafin sada zumunta na Facebook
Wani matashi mai suna Muhammad wanda ya riga mu gidan gaskiya bayan da aka cire masa ƙodarsa domin a sakawa mahaifiyarsa.
Tun da farko dai mahaifiyar Muhammad ta kasance tana fama da ciwon ƙoda, hakan yasa likitoci a asibiti suka sanarwa da iyalanta cewar dole sai an canza mata ƙodarta sakamakon sun dai na aiki.
A ƙoƙarin ceto ran mahaifiyar tasa, Muhammad ya aminta ya bayar da tasa ƙodar guda ɗaya a sakawa mahaifiyar tasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matata Ta Tsunduma Rayuwata Cikin Bakin Ciki – Miji Ya Fadawa Kotu
Bayan gwaje-gwaje da likitoci suka yi, sun aminta da Muhammad ya bayar da tasa ƙodar domin a sanyawa mahaifiyar tasa.
Sai dai Allah cikin ikonsa, bayan da aka kammala aikin cire kodar ta Muhammad aka kuma sanyawa mahaifiyar tasa, sai Muhammad Allah ya yi masa rasuwa.
Ya rasu a lokacin da ita kuma mahaifiyar tasa take a raye yanzy haka.
Jaridar Zuma Times ce ta wallafa wanna\n rahoton a shafinta na sada zumuntar zamani ta Facebook.
Labarin ya ja hankalin dayawa daga cikin masu amfani da shafin na majiyar tamu, inda muka ciro muku wasu daga cikinsu.
@Bello Galadanchi ya ce: Allah Kabashi Ladar Wanga Aikin Alkairi Dayayi
@Bin Kabeer ya ce: Allah kajiqanshi da rahma dan albarkacin al qur,an
@Mikail Abdulkadir ya ce: Allah yajikan shi da rahma
@Zaharaddeen Isah Presdor ya ce: Wannan shine cikakkiyar sadaukarwa. Allah ya jikansa yasa yana Aljannah
@Ummalkhayr Umar ta ce: Allah ya jikan shi Ya saka ma shi da aljanna Firdaws
@Sakeenarh Sarleh ta ce: Allahu akbar allah ubangiji yajikashi yasa ya huta Allah yasa aljannah ce mako mansa
@Hamisu Shehu Kazaure ya ce: Ubangiji Ta’ala Ya ba shi gidan Aljannah. Lallai wannan an yi ɗan arzuƙi, irin albarka. Allah Ya ba mu ‘ya’ya masu ƙaunar mu irin wannan yaro.