Majalisar dokokin jihar Oyo a ranar Talata ta dakatar da shugaban karamar hukumar Irepo Sulaimon Adeniran wanda aka fi sani da Santana bisa wasu zarge-zarge da ake yi masa.
Kakakin majalisar, Adebo Ogundoyin ne ya bayyana hakan a yayin zaman da ‘yan majalisar suka yi,Vanguard ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwata-Kwata ‘Yan Najeriya Ba Su Yi Amanna Da Yan sanda ba– Shugaban Hukumar ‘Yan sanda
An bukaci mataimakin shugaban karamar hukumar Joel da ya karbi ragamar tafiyar da harkokin gudanarwar karamar hukumar.
Joel zai cigaba da rike ragamar har zuwa lokacin da kwamitin da aka kafa domin binciken zargin da ake yi wa shugaban karamar hukumar zai kammala aikin sa.
A wani labarin kuma, Karfin hali: An Cafke Wani Yaro Daya Sace Wata Motar Bas
Hukumar ‘yan sanda ta Nashville babban birnin jihar Tennessee dake kasar Amurka ta samu nasarar kame wani matashi da ba a san ko wanene ba, bisa satar wata motar bas ta makaranta, a wani yunƙuri na arcewa da ita,Punch ta rahoto.
Yaron, mai shekaru 14, ya hau motar bas din ne daga makarantar Kipp College Prep da ke unguwar Antioch kuma ya yi tafiya a hankali a yammacin Nashville a ranar Asabar, da misalin karfe 4 na yamma.
A cewar hukumar ‘yan sanda ta Metro Nashville, yaron ya yi hanyarsa ta zuwa wani gidan mai inda ya samu famfon mai na Gas ya zuba a wani yunkuri na tserewa da motar ya ci karo da wani mai tafiya a kasa.
Sai dai ba a san manufarsa ba a lokacin da ‘yan sanda suka fara binsa, amma ya ci gaba da tafiya inda ya bugi wata mota yayin da yake kan titin I-40.
A ƙarshe, jami’an sun sami damar tsayar da bas ɗin, inda suka fasa tagogin motar tare da kame yaron.