Yadda Ɗan Sarki, mai shekaru 32, ya lashe zaben cike gurbi a Taraba
Sadiq Tafida na jam’iyyar PDP ya zama zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jalingo/Yorro/Zing a jihar Taraba.
Tafida, mai shekaru 32, wanda ya samu jimillar kuri’u 19,681 da ya samu a zaben da aka sake gudanarwa a ranar Larabar da ta gabata, dan Sarkin Muri ne, Alhaji Abbas Njiddah Tafida.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yadda Shettima ya nemi Fubara ya gaida Wike a taron fadar shugaban kasa
Da yake bayyana sakamakon zaben a ranar Alhamis, jami’in da ya lashe zaben, malami a jami’ar Wukari, Farfesa Olarenwaju Oladipo, ya ce dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 19,681 a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a Taraba.
Innocent Jabayang na jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, ya zo bayansa da kuri’u 16,379, yayin da Aminu Malle na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 12,662.
Zaben wanda jami’in zaben ya ce an fafata sosai, kuma dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Aminu Liman ya samu kuri’u 3,646.
A ranar 3 ga watan Fabrairun 2024 ne aka sake gudanar da zaben dan majalisar wakilai a jihar, amma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana rashin kammala zaben.
A wani labarin kuma:Ba zan taɓa amince wa a shigo da abinci daga kasashen waje ba’ – Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai amince da shigo da abinci ba ko kuma ya kafa hukumar kula da farashi.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din da ta gabata, bayan wata ganawa da ya yi da gwamnonin jihohi 36, da ministan babban birnin tarayya, mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, da kuma darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, a Abuja.