Wani dan Najeriya ya bayyana tashin hankalin da wani mutum ya shiga bayan matarsa ta sanar da shi cewa yaransu biyu ba nashi bane, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda @MeverickThamani ya bayyana a shafinsa ba Twitter, mutumin ya kai shekaru 50 da doriya kuma ‘yar uwarsa ce yanzu haka take kulawa da shi a asibiti sanna ita ce ta bayar da labarin abinda ya same shi.
KU KARANTA ‘Yan baranda sun farmaki ayarin Atiku an kwantar da mutane da dama a asibiti
Ta ce mutumin yana matukar kaunar matarsa wanda hakan yasa ya zabe ta a maimakon ‘yan uwansa. A bayan har yanke alaka yayi da ‘yan uwansa sai daga baya ya kama ta tana lalata da wani namiji.
Wannan ne ya janyo rikici ya barke tsakaninsu har ta kai ga sanar da shi cewa yaransu ba nashi bane. Ana tsaka da rikicin ne ta bayyana masa wannan mummunan labarin wanda yasa ya fadi kasa bayan ya yanke jiki, hakan yayi sanadiyyar shanyewar barin jikinsa.
Bayan ganin halin da yake ne matar ta tsere ta kwashe kudi daga asusun bankinsa tare da guduwa da yaran. Yanzu haka yana zama ne karkashin ‘yan uwansa inda suke kulawa da shi kamar yadda mutumin ya bayyana a Twitter.
Buhari Zai Kaddamar Da Asibitin Shugaban Kasa Na VIP Daya Lashe Naira Biliyan 21 A Abuja
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da bangaren shugaban kasa na VIP a asibitin fadar gwamnati dake Abuja.
Asibitin wanda aka gina tare da samar da kayan aiki a kan kudi naira biliyan 21, an kwatanta reshen VIP a matsayin wani aikin sadaukarwa ga gwamnatin Buhari.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha, ya kaddamar da sabbin ayyuka guda hudu a asibitin ranar Alhamis.