Wata ‘yar Najeriya cike da takaici da alhini a dandalin TikTok inda ta bayyana yadda babbar kawarta ta kwace mata saurayin da take matukar kauna, Legit.ng ta ruwaito.
Budurwar mai suna Princess Toria ta bayyan a wani gajeren bidiyo wanda ta wallafa ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba inda tace kawarta ta yi mata wuff da saurayi.
A cewar Princess, ta dawo Najeriya ne don ta bai wa aminiyarta mamaki hakan yasa bata sanar da ita batun zuwanta ba, ashe zata tarar da labari mai firgitarwa.
Kamar yadda tace, kawarta za ta yi aure don ana shirin da rana, hakan yasa taga dacewar taje tayi mata kara.
Sai dai abinda yafi daure mata kai shi ne yayin da taje shagalin da ranar, ta tarar da saurayinta ne angon.
Ta bayyana yadda ta gano ashe kawar tata ta haifi yaro mai shekaru biyu da saurayinta ba tare da saninta ba.
Labarin ya bayar da mamaki ga mutane da dama yayin da wasu ke ganin dakyar hakan ta yuwu. Princess ta wallafa hotunanta yayin da take barin filin jirgin Najeriya.
KU KARANTA: Ka dawo min da budurcina, ƴar Najeriya ta buɗe wa saurayinta wuta bayan sun rabu
Wani matashi ya mayar wa tsohuwar budurwarsa amsa bayan sun rabu kuma ta bukaci ya mayar mata da budurcinta, Legit.ng ta ruwaito.
Wannan amsar tasa ta ba mutane da dama mamaki. Da farko ta bukaci ya dawo da ita yadda ya ganta, inda shi kuma ya bukaci ya dawo masa da kudadensa da ya dinga kashe mata lokacin su na soyayya.
A cewarta da farko ta yi tunanin soyayyar tasu za ta kai ga aure ne, shiyasa ta saki jiki da shi. Ta kara da tuna masa yadda ta zauna da shi a lokacin da ba ya da kudi inda ta fuskance shi bayan gano yana ha’intarta.