Wata magidanci ɗan Najeriya ya bayyana yadda matar sa tayi masa wayau take sanya shi yin aikin gida.
Magidancin wanda yake amfani da sunan @MaxOfLagos Twitter, ya bayyana cewa matarsa ta kawo tsarin biyan tarar dala ashirin ($20) ga duk wanda ya kasa gama ayyukan da zai yi a rana.
KU KARANTA KUMA: Matasa Sun Kwashi Guzuri Sun Tare a Banki Suna Dafa Abinci Yayin Jiran Cirar Kuɗi
Ya bayyana cewa ya gano matarsa bata son kammala ayyukanta duk kuwa da cewa itace ta kawo wannan tsarin.
Daga nan sai ya fahimci cewa wannan wata dubarar ta ce ta ganin ta sanya ya riƙa yin ayyuka da yawa yayin da ita kuma take biyan tarar.
A kalamansa:
“Da ni da matata muna da tsarin biyan tara kan aikace-aikacen gida, biyan tarar dala ashirin ($20) idan baka kammala aikin ranar ba. Wannan shawarar ta ce amma na lura tafi yawan karya wannan dokar.”
“Sai yanzu na gano ashe biyana take yi na zama ɗan aiki saboda bata damu da biyana tarar ba.”
Wannan rubutun nasa ya janyo cece-kuce a tsakanin mutane da dama a yanar gizo, inda wasu suka riƙa shawartar sa da ya ƙara kuɗin tarar ta yadda dole matarsa ta riƙa yin aikace-aikacen gidan.
Sai dai magidancin yayi martani da cewa:
“Wasu daga cikin ku na cewa na lallaɓa a ƙara kuɗin tarar. Da ƙyar nake iya biyan na yanzu, zaku taimaka min idan aka ritsa da ni?”
Duk Da Bani Bace Zaɓin Mijina, Ya Aureni Saboda Ban Tatse Masa Aljihu -Matar Aure
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta bayyana dalilin da ya sanya mijinta ya aureta duk da ita ba zaɓin sa bace.
Wata matar aure ƴar Najeriya ta bayyama ccewa lokacin da zata auri mijinta, ta san cewa ba ita bace irin matar da yake yayi rayuwa da ita.
Ta bayyana cewa duk da dai mijin nata bai fito fili ya gaya mata ba, ta fahimci cewa yafi son samun ƴar ƙwalisa a matsayin matar aure.